Ba Dukkan Shaiɗanu Ake Ɗaurewa Ba Acikin Watan Ramadan

 Ba Dukkan Shaiɗanu Ake Ɗaurewa Ba Acikin Watan Ramadan baYabbata cewa ana ɗaure shaiɗanu a lokacin da Ramadan ya shigo, amma ana ɗaure manya-manyan shaiɗanu ne, ana ƙyale kananu.

        Hakan yasa idan mace tana da iska ajikinta koda a lokacin Ramadan ne suna iya tashi, saboda shi wannan Aljanin dake jikinta ƙaramin shaiɗani ne, ba babba ba,baya daga cikin wamda ake ɗaurewa.

        Haka kuma idan kana sallah zakaji baka rabuwa da wasi-wasin shaiɗan, to suma waɗannan shaiɗanun da suke zuwa suna sakawa mutum tunani acikin sallah ba'a ɗauresu, saboda suma ƙananun shaiɗanu ne.

       Sudai waɗannan ƙananun shaiɗanun sune suke haddasa rigima tsakanin mijin da mata a cikin watan Ramadan harma akai ga mutuwar aure.

        Sune waɗanda suke hana mutune zagewa akan ayyukan alkhairi acikin watan Ramadan, su rinƙa sawa mutane kasala, kuma suke jefawa mai Azumi sha'awa harma wani yakai ga karya Azuminsa.

        Sune malaman tsubbu ke amfani dasu acikin watan Ramadan, sai suce ai Ruhanai ne, to ai duk Aljanin da mutum zai kirashi yazo kuma yasa Aljanin aiki yayi koda musulmi ne Aljanin, to baya tsoron ALLAH shaiɗani ne, domin kuwa Aljani mai tsoron ALLAH baya amsa kiran kowa inba na ALLAH ba.

        Sune waɗanda idan da mace ko namiji zai kwanta bacci da rana ko dare acikin Ramadan, sai yazo masa da siffar mace ko namiji, taganta ana saduwa da ita, to wannan mai saduwa da mutum acikin baccinsa shima ƙaramin Aljanine.

        Sune wanda inda zaka shiga banɗaki babu addu'a zai iya shiga jikinka ya rinƙa cutar dakai, manyan shaiɗanun Aljanu basa zama a banɗaki sai ƙananu, su kuwa ƙananun shaiɗanun ba'a ɗauresu cikin Ramadan.

        Don haka zamu ga koda acikin watan Ramadan ana saɓawa ALLAH, sai dai ba kowa ba, saboda su manyan suke umartar ƙananun da tunzura mutane akan saɓon ALLAH,.

       Su manyan sune suke shan jinin mutum kona dabba, suke sawa ana zubar da jini, ana kashe rayuka, shiysa idan Ramadan yazo ake samun sauƙin kashe-kashen rayuka, hatta ƴan ta adda sukan saurara sai bayan Ramadan, saboda manyan shaiɗanun dake shan jini an ɗauresu, dama kuma sune ke tunzurasu su kashe rayuka.

        Amma da zarar an ɗauresu, suma ƙananun Aljanun basu samun ƙwarin gwiwa sosai, sai dai suna zuwa su sawa mai sallah was-wasi damai karatun Alƙur'ani su sashi hamma dssr.

        Don haka kada mu shagaltu da wasa da azhkar na neman tsarin ALLAH daga shaiɗanun Aljanu da mutane koda acikin Ramadan ne.

ALLAH ka karemu daga sharrin shaiɗan babba da ƙarami.

ALLAH ka gafarta mana zunubanmu baki ɗayanmu Ameen.

Post a Comment

Previous Post Next Post