Yadda Ake Gane Fake Alart A Kowacce Irin Waya
Fake Alerts zai yawaita a wannan tsarin na Cashless Policy.. Ga yadda zamu gane Fake Alerts...
Wannan tsarin da akeso a tabbatar dashi a wannan ƙasar tamu na Cashless Policy zaizo da abubuwa da dama musamman Cyber Crime irinsu Fake Alert, kutsen asusun banki makamantansu, dan haka dole mu koyi sanin yadda zamu gane waɗannan abubuwan domin kare kawunan mu da faɗawa hannun macuta kuma yan damfara, tun kafin Nigeria tashiga wannan tsarin na Cashless andaɗe anayin Fake Alert kuma an daɗe ana cutar mutanen mu yan kasuwa da wannan tsarin musamman masu POS.
Akwai hanyoyi guda biyu da suke bi wurin yin wannan Fake Alert, hanya ta farko mai sauƙi ce wurin yi kuma mai sauƙi ce wurin ganewa, hanya ta biyu itace mai wahala wurin yi kuma mai wahalar ganewa, hanya ta farko suna amfani da kusancin dake tsakaninka dasu ko kuma samun damar karɓar wayarka suyi saving Number wayarsu a cikin wayarka da sunan bankin da kake amfani dashi.
Misali: Zasu karɓi wayarka sai suyi Saving Number su da sunan bankin da kake amfani dashi kamar First Bank haka bayan wani lokaci sai su shiga cikin wayarsu su nemo ainahin Credit Alert da banki suka taɓa tura masu sai su shiga suyi Copy nasa, suyi Editing su cire Time na Message ɗin su sanya daidai lokacin da zasu turo maka Message da sauran abinda yakamata su cire sai su tura maka.
Kai kuma yana zuwa batareda ka duba Balance ba, da zaran kaga sunan bankinka tareda rubutun Alert sai kawai kayi tunanin dagaske Real Alert ne.
Hanya ta biyu akwai Website da Application da ake amfani dasu wurin yin Fake Alert amma wannan hanyar ta waÉ—anda suka É—auki abun sana'a ne wato waÉ—anda sukeyin abun dagaske, kuma irin waÉ—annan hanyoyin sai ma kabiya kuÉ—i sannan zasu baka damar kayi amfani da ita wurin yin Fake Alert É—in, acikin Application É—in akwai "Cardro Pro v8.5" da kuma websites kala-kala da akeyin Bulks Message, ta amfani da wannan Application É—in idan zasu turo maka sakon Alert bazasu turo da Complete sunan banki ba, kamar idan zasu saka Sterling Bank sai sun saka Starling bank kaga Instead of su saka "E" sai suka saka "A" ko kuma idan First Bank ne sai su saka Fir$t bank, a maimakon su saka letter "S" sai su saka dollar sign ( $ ) ko UBA kuma sai su saka VBA, a maimakon "U" sai su saka "V" idan baka lura ba a haka zaka gani sai kayi tunanin Real Alert ne tunda daman ka riga da kasan cewa Bank idan suka turo maka da Alert yana zuwa batareda baka damar kayi Reply ba to suma ta amfani da irin waÉ—annan Applications É—in Alert zaizo batareda baka damar kayi Reply ba.
Note: Irin wadannan Applications din babu su a Playstore saboda Playstore baya ajiye Applications da zasuyi Harming mutane, dan haka sanin sunanta bazai baka damar ka iya gano inda zaka sameta ba.
Taya Zan Gane Alert Ɗin Ƙarya...?
Abun na farko É—an'uwa Idan banki suka turo Messages ba'a masu Reply. Zakaga a wurin reply É—in sun rubuta "Sender Doest Not Support Replies". Abu na biyu ka duba sunan Bankin daga cen sama ka tabbatar sunan ba Mistake a jiki, abu na ukku Idan kaga Alert É—in yazo daban a maimakon yazo tareda sauran Alert É—in da kake dasu a akwatin message É—inka ya jeru dasu bawai ya ware kanshi ba. Misali idan ka duba Alert É—in da bankinka sukeyi maka duka Alert É—in suna zuwa ne a Box É—aya, wato a layi É—aya babu wani Message da suke jeruwa dashi, to shi Fake Alert ware kanshi yakeyi daban.
Babbar hanyar gane Fake Alert shine idan bakaga Alerts message É—in a cikin jerin Alert É—in da kake recieving ba da kuma ya kasance kana Checking Balance domin tabbatarwa.
Allah ya tsare mu..
0 Comments