Yadda Zakiyi Ki Kara Kiba Jikinki Yayi Ɓulɓul Cikin Sauki
BAYANI YADDA ZAA KARA KIBA GA MAI BUKATAR WANNAN.
(1) Domin Karin kiba Za'a samo Zabib,da hulba, Za'a wanke Zabib din sannan azuba shi acikin ruwa Kofi biyu, sai shi yayi awa (16) Sannan Amur tsike shi a tace bayan ya hade sai kuma a zuba hulba cokali (2) idan ruwan yayi kasa Sai a kara wani daga nan sai asanya a freeze a rufe amma banda marfin Wanda zai rufe kwanon ko robar gamgam. Idan yakara kamar awa (6) Sai a tace za'arika shan karamin kofin shayin larabawa ko buzaye.
Sai dai yakan sanya kara cin abinci, to ana bukatar a rika cin abinci mai kyau wanda yake gina jiki.
(2 ) Za'a samo zabib Kofi biyu, a wanke sosai sannan a zuba ar uwan a kalla kamar Rabin Lita zuwa Lita daya sannan a zuba garin hulba mai kyau Kofi daya sai a zuba a kalla zaiyi awa 12-18 ko dare cikakke daganan za'a tace a zuba a waje mai kya sai a rika shan karamin Kofi sau 3-4 arana.
Sannan sai a rikacin kwaya goma sau 3 a rana insha Allah za'ayi wannan hadin sau 2-3 ya isa, insha Allah zaayi mamaki sosai, wannan anjarraba angwada kuma antabbatar.
Sannan cin zabib yana magance sihir da kuma matsalar shaidanun aljannu, cinsa kuma yakan zama asamu kariya daga sihir, ko shafar jinnu.
Hhanya ta biyu:
{1} Ya yan hulba
{2} Alkama
{3} Waken suya
{4} Gyada
{5} Garin dabino
{6} Garin farar shinkafa
{7} Madara
{8} Zuma
Saiki maida su gari suyi laushi. saiki rika diba cokali daya ana soya kwai dashi .man suyar yakasance danyan man zaitun ne. yadda za'a sarrafasu zaki samu alkama da farar shinkafa ki jikasu sai sun kwana saiki shanyasu subushe
sannan ki kai anika.sannan kisamu garin dabino sannan gyadama a soya ta
Sama samansa sannan ki nikata saiki hada garukkan waje guda sannan kidebi cokali 2 ki zuba ruwan rabin kofi sannan ki dora akan wuta harya tafasa
Saiki sauke kisa madara ta ruwa kota gari da zuma saiki hada kirinka sha musamman idan zaki kwanta barci cikin kankanin lokaci zakiyi kiba sumul fatarki ta canza._
QARIN GIRMAN KUGU KUNKURU.
Zaki samu wadannan kayan lambun
{1} Abarba
{2} Ayaba
{3} Gwanda
{4} kankana
{5} Zuma
{6} Madara peak
Saiki hadasu guri guda ki markadasu su zama ruwa saiki zuba zuma da madara kirinkasha. sai kuma ki samu zogale dafaffa ki hada da alaiyahu ki zuba tumatir da albasa kiya kwadon wato datu haka zaki rinka yi ga kwadon. ki rinka yin wannan kayan lambu da kika markadasu sai ki rinkasha da a suba
Post a Comment