Yadda Zakayi Chatting Da Kowanne Yare Ta Hanyar Amfani Da Google Keyboard Ba Tare Da Ka Mallaki Dictionary Ba.

 Yadda Zakayi Chatting Da Kowanne Yare Ta Hanyar Amfani Da Google Keyboard Ba Tare Da Ka Mallaki Dictionary Ba.

Assalamu alaikum 'yan uwa da abokai barkanmu da yau barka da kasancewa da SIRRIN ANDROID.


Yan'uwa yau wani application na keyboard na kawo mana ga duk masu yin amfani da wayar android da iphone. Application ne zai baka damar chatting da kowanne kalar yare koda bakajin wannan yaren.


Idan kanada wannan keyboard a wayanka baka bukatar dictionary domin fassara wani yare domin shi kanshi dictionary ne.


Wannan keyboard din mallakin GOOGLE ne kusan kowa yasan miye google, keyboard din yana dauke da yaruka masu yawa.


Danna wannan link din domin sauke App din

👇 

Danna Download Domin Sauke Google Keyboard 

DOWNLOAD 


Amfanin wannan keyboard din shine zaka saita shine a wayar ka nomal kamar yanda kakeyin typing na chatting ko message a wayarka.


Sannan a jikin keybord din zaka zakaga yaruka da yawa sai ka zabi yaren da kakeso kayi magana da shi, duk yawan su zaka iya amfani da kowanne. Domin saukaka ma rubutawa ko fassarawa.


To da zarar wani ya turoma sakon maganar da ba yaren ka bace shi wannan keybord zai baka damar fassara zuwa yaren da kake so. Bayan wannan zaka rubuta magana da yaren da ka ga dama shi wannan keybord zai juya ma zuwa yaren da kake so ka turawa wanda kukeyin chatting din.


Kuma ba wai iya whatsapp bane wannan hanya take ba aa ko a ina ne duk inda keybord din ka ya fito kuma zakayi rubutu a gurin to normal zaka iya fassara ko ka rubuta abinda kake so.


Allah yasa mu dace

Post a Comment

Previous Post Next Post