Yadda Chiwon Infection Yake Nakkasa Jikin Macce Da Yadda Ake Magancewa

 Yadda Chiwon Infection Yake Nakkasa Jikin Macce Da Yadda Ake Magancewa

 



Allah Ya halicci ko wacce mace da daɗinta da kuma ni’imarta. Sai dai ace wata tafi wata, amma in har lafiyansa kalau to in namiji yayi amfani da shi zai samu biyan bukatarsa. Amma cututtukan al’aura ne suke mutukar lalata jikin ƴa mace. Sai mace ta ɗauka ita ce ba tada daɗi yasa mijin baya jin dadinta. Idan har jikin mace babu ko wane ciwo na al’aura to abubuwa kaďan zata ci ko ta sha sai ni’ima ya sakko mata mijinta ya gamsu da ita mutuƙa.


Ciwon sanyi wani abu ne da ya zama game duniya a duniyar matan yanzu. A cikin kashi 100% na mata 5% ne kawai basu da shi. Wannan kuwa ya haɗa da matan aure da ƴan mata. A rubutu da yawa mata suna bayanin illolinsa da kuma haɗarinsa ga rayuwar mace. Idan ke budurwa ce to in kika bar shi har kika yi aure zai iya hana ki jin daɗin aure gaba daya. Zaki dauƙi shekara da shekaru baki san menene daɗin saduwa ba. Kuma zai iya cire miki sha’awa kwata-kwata. Haka nan zaki yaɗa wa mijinki da kishiyoyinki in kina da su wanda in suka samu yin maganinku tare zai wahala, musamman maza da basa son shan magani. Kin ga sai ki yi ta wahala kina kashe kuɗi yana dawowa saboda na waɗancan bai mutu ba.


Idan ke matar aure ce zai cire miki dukkan daɗin jikin ƴa mace. Kuma ko kin yi maganin matan miliyan ba zaki kai daɗin wacce ba ta da infection ba in ma yayi aikin kenan. Zaki yi ta asaran kuɗi amma wallahi ba zaki yi daɗi ba. In ya fara shahara zai rinƙa sanya ɓarin ciki, daga nan kuma ya hana ki ɗaukan ciki gaba ɗaya. Mijinki zai iya tsanarki ko jin haushin ki saboda infection ya cire miki dukkan ni’imar jikin mace.


Kaɗan daga cikin alamominsa:


1.Fitan ruwa, wanda zai iya zuwa kamar ruwa amma yellow ko green tsinkakke. Ko kuma ya fito a fari ko in ce milk mai kauri sosai.


2.Wanda wannan ruwan zai haddasa miki ƙaiƙayi a al’aurarki har ma da jikinki wani. Ki yi ta susa har wurin yayi ja. Haka nan in ya fara shahara sai ruwan ya fara wari mai tada hankali.


3.Daga nan sai ya feso miki da kuraje masu azabar ƙaiƙayi. Wanda in ya tsarga in baki wasa ba ko a cikin jama’a ne sai kin sosa.



4.Ciwon mara da baya, wani ma yana sanya ciwon kai, jin amai, ko yin laulayi kamar mai ciki.


5.Dashewar gaba ki ji kamar kin ƙone, haka nan zaki ji kamar ana tsungulinki a cikin al’aurarki da wajensa.


6.Bushewar gaba koda ke budurwa ce zaki jiki a bushe a bushe. Matar aure kuma saukar ni’ima sai ya rinka mata wahala koda ta sha abun ni’imar.


7.Ɗaukewar sha’awa gaba ɗaya ko kiji kina yi kaɗan kaɗan. Kuma duk wani abun da zaki ci da ya kamata ya saukar miki da ni’ima zaki ga ke baki ganin komai.


8.Jin kamar tana ko tsutsa yana miki yawo a mararki ko ki ji motsinsa a gabanki.


9.Fashewar kafa, ki ga kullum ƙafarki akwai faso ko kauje wani infection ne ke sakawa.


10.Rikicewar al’ada koma rashin zuwansa gaba ɗaya ko sanya miki ciwon ciki. Ga mutuƙar buɗe mace ga budurwa ko matar aure, zaki yi ta neman maganin tightening amma ko kin yi zaki buɗe saboda infection. Dama wasu da babu adadi ko wacce da kalar nata.


11. Kumburewar gaba. Da wasu abubuwa da zai iya samunki. Wannan ya danganta da yanayin jikinki ko yanayin yanda ya dade yake ta shahara.


Kada wai ki ji kunya ki ɓoye don kina da shi in ma ke matar aure ce ko budurwa, domin wannan halin mata ne. Mata da yawa na da shi to menene zai sa ke ki boye cuta? Yawanci maganin asibiti sumar dasu yake yi ko in ce baya kashe su duka in ba kin yi mugun nacewa bane. Haka nan koda ya warke in baki bi ka’idoji ba still zai dawo. Saboda mafiya yawan mu zamu warke amma ba zamu yi wa kan mu fada ba, sai mu koma akan wannan bad habit din. To kullum kuwa kudin ki zai kare wurin amsan maganin infection. Wani ma ya cuce ki ya baki fake, wata kuma gaba daya ta cinye kudin taki turo miki da kayan. Allah Ya warkar da masu fama da shi ya basu lafiya.


SIrrin RIke GIda 

Post a Comment

Previous Post Next Post