Ingantaccen Maganin Gyaran Nono Ya Mike Tsaye Yayi Taushi Kamar Fulawa

 Ingantaccen Maganin Gyaran Nono Ya Mike Tsaye Yayi Taushi Kamar Fulawa 

Assalamu Alaikum Warahmatullah


GYARAN NONO A MAHANGAR LIKITA (TIGHTENING OF SAGGING BREASTS)


Wannan rubutun na taba turo shi a cikin wanna gidan mai albarka a ranar Talata 19 ga watan January, 2021, kuma nayi sa’a admin ya sake shi domin members su karanta. Dalilin da yasa nayi rubutun shine babban jigonmu, Dr. Kabir Yusuf Danwurin Dutsi, yayi posting din tambayar da wata member a tayi, wacce take neman ayi bayani game da yadda maza a cikin mu sukan rudu da sigar jikin matan turawa wadanda ake nuna su a cikin fina-finai. Mafi yawan lokaci akan nuna cewa nonuwan matan turawa a tsattsaye suke basu faduwa, ko da kuwa matan tsofaffi ne. kuma maza a cikinmu suna nuna matukar sha’awarsu akan irin wannan siga, ta yadda har sukan ingiza matanmu suna yin fadi-tashi wajen ganin sun sami irin wannan sigar, watau nonuwansu su kara girma kuma su kasance a tsattsaye domin su burge mazansu. Matanmu suna yin haka ne ta hanyar amfani da magunguna na bature (orthodox medications) ko kuma magungunan gargajiya (herbal medications). Allahu Akbar! wallahi matanmu suna kokari, Allah ya saka musu da alkhairi.


To, sai kuma naga Dr. Kabir din ya saki wani post a ranar Alhamis dinnan 29 ga watan December, 2022, wacce wata member mai suna Aneesa Ibraheem Matawalle tayi domin neman sanin abinda ya kamata tayi amfani da shi a likitance domin nonuwanta su cicciko su tsaya saboda an fada mata cewa yin amfani da magungunan gargajiya suna iya haifar mata da illa ga lafiyarta.


Daga nan fa sai members sukayi caa akanta. Wasu suna ganin rashin kunyarta, wasu kuma wautarta, wasu kuma rashin wayewarta, da dai sauransu. Ya zuwa yanzu da nake yin rubutun nan, post din Aneesa Ibraheem Matawalle ya sami comments guda dari da daya (101), da kuma likes casa’in da biyar (95). A fahimta ta yakamata da ita mai tambayar da kuma mu masu karantawa da comments muyi wa juna uzuri. Bai dace ba mu rika yin bakaken maganganu ga masu tambaya ba, ko da kuwa bamu ga dacewar tambayar ba. Idan bamu san amsa ba, to, sai mu bari wanda ya sani yayi bayani. Kuma abinda ya kamata mu sani shine yin tambaya kowace iri ce yana sanya likitocin su yi bincike, domin kila basu ma taba yin tunani akan tambayar ba.


HALITTAR NONON MACE (WOMAN BREAST ANATOMY)


Nonuwa wasu halittu ne guda biyu wadanda suke tsirowa a kan kirjin mace. Duk da kasancewar namiji shima yana da nono, to, amma bashi ake magana anan ba. Nonon mace halitta ce wacce ta kunshi curin tsoka(tissue), kitse (fats), kananan bututu (ducts) da jijiyoyin jini (veins). Saidai kitse da jijiyoyi sunfi yawa a cikinsa. Wannan ne ma ya sanya cewa girman nonon mace ya danganta ne da yawan kitsen da yake cikinsa. Nonuwan mace suna fara girma ne daga lokacin da ta isa balaga (puberty) wanda yake farawa daga shekara 12 zuwa sama. Nono ya kunshi wasu kananan jakunkuna dunkulallu (lobes) kimanin 15 zuwa 20, wadanda sune suke samarwa da kuma adana ruwan nono (breast milk). Kowace jaka ta ruwan nono tana da bututu wadanda suka hadu da juna, kuma ta cikinsu ne ruwan nonon yake biyowa ya fito waje ta hanyar kan nono (nipple) wanda shi kuma yake a saman nono. Kan nono yana kewaye da wani shashi mai duhun launi (areola) kuma akwai wasu kananan abubuwa a kansa masu kumburi kamar kuraje (areola bumps). Amfanin wadannan kurajen shine suna samarda maiko wanda yake sanya kan nono ya zama mai laushi kuma ya sami kariya daga kwayoyin cututtuka (infection). Kuma areola yafi amfani a lokacin shayarwa, domin shine yake tattaro ruwan nono ya fito da shi waje. Nono yakan samu siffarsa ne ta kasancewa a tsattsaye (breast firmness) idan jijiyoyinsa da tsokarsa suna damfare da juna sosai, kuma hakan yafi samuwa a lokacin kuruciya. Domin haka idan shekaru suka fara nisa wannan damfarewar ta tsoka da jijiyoyi takan rage, daga nan sai nono ya zube (sagging).


MATSAYIN NONON MACE A WURIN NAMIJI


Bincike ya tabbatar da cewa nonon mace yana daya daga cikin abubuwa masu matukar tasiri wajen kaukar hankalin da namiji zuwa gareta, musamman a lokacin saduwar aure. Wannan ne dalilin da yasa al’ummomi da yawa suke alakanta nono da jima’i (sexual), ta yadda ba’a cika son ayi magana kiri-kiri a kansa ba, sai idan ya zama dole. Al’ummar hausawa ma tana da wannan fahimtar. Sa’annan la’akari da tasirin nono ga namiji ne ya sanya mata suke yin kokarin gyaran nononsu domin su janyo hankalin mazansu. Wannan al’marin haka yake a tsakanin duk matan duniya ba namu na Nigeria kawai ba. Saboda haka Aneesa Ibraheem Matawalle batayi laifi ba domin tayi tambayar yadda nonuwanta zasu cicciko. Abinda take bukata shine a wayar mata da kai a ilmance kuma cikin lafazi mai taushi.


GYARAN NONO TA HANYAR AMFANI DA MATAKAI NA LIKITANCIN ZAMANI (ORTHODOX MEDICATION)


Hanyoyin da mata suke amfani da su wajen gyaran nono (watau karin girmansa da kuma tsayuwarsa) sune:


1. Kawayoyin magani (breast enhancement pills): wadannan sune kwayoyin maganin da aka sarrafa su a likitance (pharmaceutical drugs), kuma sune ake kira vitamin supplements. Mata a cikin wannan group din suna yawan tambaya akan ingancinsu. Kwayoyin suna dauke ne da sinadarin estrogen wanda yake kara girman nono. Sauran abubuwan da ake sanyawa sun hada da barley (sha’ir), fenugreek (hulba), oats (hatsi), palmetto (dabino), dong quai (wani itace ne da ake samunsa a China), blessed thistle, pueraria mirifica, fennel seed, hops, bovine ovary extract (duka ban san sunayensu da hausa ba). Bincike ya tabbatar da cewa kwayoyin kara girma da kuma tsayuwar nono suna da illa, musamman idan an dade ana amfani da su. Misalin wadanddan kwayoyi sune Lady Capsule, BustMaxx, Curves Capsules, Curvinexx, Pueraria Mirifica 3000, Natural Pueraria Mirifica, IsoSensuals Enhance da sauransu.


2. Mayukan shafawa (breast enhancement creams): wasu daga cikin ire-iren wadannan mayuka sune Divine Derriere Breast and Butt Enhancement Cream, COS Naturals Breast Plumping Lotion, NanoMed Finale Bust Cream, Diva Fit N' Sexy Breast Cream, True Level Breast Plumping Lotion, Must Up Bella Cream Breast Enhance Cream, Liduoliya Breast Enhancement Frost, Breast Full Intensive Breast Enlargement Cream, Miracle Bust Cream, Eveline Slim Extreme 4D Intensive Serum.


3. Allura (breast enhancement injections): maimakon shan kwayoyi ko kuma shafa mayuka na gyaran nono, wasu matan sukan yi allura a nononsu. Dalili shine ita allurar tana shiga cikin tsokar nonon ne kaitsaye domin ta bayar da tasirin da ake bukata. Allurai da ake amfani da su sun hada da Botox, Vampire Breast Lift, Hyaluronic Acid (Ha)-based Dermal Fillers da sauransu.


4. Aikin tiyata (breast enhancement surgery): wannan yana nufin yanka nono a cikin dakin tiyata domin a rage yawan kitsen da yake cikinsa, ko kuma ayi dashen wata jaka a nonon wacce take dauke da ruwa mai kauri (cohesive gel implants). Jakar ce zata baiwa nono siffar tsayuwa kyam kamar na budurwa. Anfi yin wannan tiyatar a kasashen waje, kuma tana da hadarin haddasa cutar daji (cancer), sa’annan ga tsada.


5. Haska nono da na’ura (laser treatment breast lift): ana yin amfani da hasken radiation domin a kone kwayoyin halittar nono matattu (dead skin cells of the breast), domin matattun cells din ne sukan sanya fatar nono ta yankwane, sai ya zube.


NAU’O’IN NONO


Kowace mace tana da irin siffar nonon da Allah ya halicce ta da shi. Wannan yana nufin halittar nonuwan mata ta bambanta. Wadanda aka fi sani sune kamar haka:


1. Cikakke kuma kewayayyen nono (round breast): irin wannan nonon halitta ne wanda maza suka fi so, domin yana da ban sha’awa, kuma a tsattsaye yake.


2. Nono daya yafi daya girma (asymmetrical breasts): wannan ba wata matsala bace a likitance, domin dama halittar jikin dan-adam ta hagu takan fi ta dama girma, ko da kuwa ba’a ganin haka a zahiri. Abubuwan da sake sanya nono daya yafi girma sosai sun hada da ciwon nono (infection), rashin daidaiton sinadarai (hormonal imbalance), rashin lafiyar halittun da suke cikin nono (developmental disorders of breast tissues), rauni a nono (breast injury), matsalolin shayarwa (breast feeding complications) da sauransu. Dukansu wadannan ana iya magance su ta hanyar shan magani, amma banda rashin lafiyar halittun nono, domin shi sai ta hanyar tiyata ake magance shi.


3. Nono mai siffar zunguru (tubular breast): wannan shine nono wanda yake da tsawo kamar zunguru ko shantu maimakon dunkulewa wuri daya, kuma akwai tazara tsakaninsu, sa’annan sashen bakin su (areola) suna da fadi sosai. Mafi yawan lokaci daya yakan fi daya girma. Irin wannan nonon halitta ne ba cuta take haifar da shi ba, kuma sai ta hanyar tiyata ake daidaita su.


4. Karamin nono (athlethic breast): shine nono maras girma, wanda da kadan ya dara na namiji girma. Wannan shima halitta ne, amma ana iya kara masa girma ta hanyar wasa da shi lokacin saduwar aure (stimulation), atisaye (physical exercise), da kuma cin abinci mai gina jiki (balanced diet).


5. Nono fiye da biyu a kirji (supernumerary breasts): wasu matan suna da nono uku a kirjinsu. Wannan matsala ce ta halitta (genetic disorder), kuma tiyata ake yi domin magance ta. Sa’annan akwai matan da suke da kan nono a cikin hammatar su amma ba zasu gane bas ai lokacin da suke shayarwa domin ruwan nono zai rika fita ta hammatar. Wannan shima ba matsala bane.


SHIN MAGUNGUNAN KARA GIRMA DA TSAYUWAR NONO SUNA AIKI?


Hakika baza ace basu aiki ba, domin matan da suke amfani da su suna ganin tasirinsu. Abinda magungunan suke yi shine suna kumbura tsoka da kitsen nonon ne kawai, sai aga ya kara girma. Amma daga bisani suna iya haddasa cutar daji ko kuma wasu matsaloli a nono. Sa’annan kuma suna takure fatar nono ne sai a gansu sun cicciko sunyi tsattsaye. Amma da zarar sun gama aikinsu (tunda ba dauwama zasu yi ba) sai fatar ta saki, kuma nonon ya kankance kuma ya sake zubewa. Da wannan nake ganin ya kamata mata su guji amfani da su, kamar yadda manyan likitocin duniya suke bayar da shawara.


ABIN LURA


Nonon matan turawa da muke gani a cikin fina-finai ba duka bane na gaskiya. Dayawa daga cikinsu implants ne. Kuma babu wani nonon da baya faduwa, sai idan lokacinsa baiyi ba. Don haka bai kamata maza su matsawa mata da cewa sai sun nemi maganin gyaran nono ba. Amma ana iya daukar wadannan matakar domin inganta lafiya, siffar, da cikowar nono:


1. Yawaita wasannni da nono tsakanin ma’aurata.


2. Yin atisaye akai-akai.


3. Cin abinci mai gina jiki.


4. Tsaftar jiki da tufafi, musamman rigar nono.


5. Yawaita amfani da rigar nono.


6. Kauce ma zafin rana.


7. Kiyaye shan magunguna barkatai ba tare da umurnin likita ba.


8. Yin ingantacciyar shayarwa ga wacce ta haihu.


Post a Comment

Previous Post Next Post